Kakakin ‘yan sandan yankin, Sergeant Enrique Carrillo, ya ce an kama wani mutum da ake zargi da kai harin.
A yau Asabar, kamfanin dillancin labaran kasar ta Korea ta Arewa, ya ruwaito cewa, shugaba Kim ne ya jagoranci gwajin wannan sabon mamaki na roka.
Ana sa ran takunkumin zai fara aiki kwanaki 15 bayan an sanar da majalisar dokokin kasar kan wannan mataki, wanda zai kai tsawon shekara guda.
Ana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da aiki, kan yadda za a shata jadawalin wannan gamayya.
An dakatar da jigilar mutane a wasu tashoshin, wanda hakan yasa mutane bin dogon layi don shiga motocin bas kyauta, don isa wasu tashoshin jirgin.
Shugaban gidan yarin jihar, Jarbas Vasconcelos, ya fada a cikin wata sanarwa cewa ‘yan wata kungiyar fursuna, mai suna Comando Classe A, ne suka saka wuta a dakunan kwanan abokan hamayyarsu na kungiyar Comando Vermelho.
Mousavi ya fadawa taron manema labarai da aka yada shi kai-tsaye a gidan talabijin na Press TV cewa, tattaunawar da kuma zaman sulhun zai yi wu ne idan aka tsara batutuwan da za a tattauna akai a kuma samu sakamakon mai kyau.
Kano Pillars ta yi nasarar buga penarti 4 ta zubar da daya, Tornadoes kuwa ta ci uku ta zubar da biyu, inda aka tashi a wasan da ci 4-3.
Wani mahari ya hallaka mutum 3 tare da jikkata wasu mutum 15 a garin Gilroy na jihar California a wajan wani bikin da ake kira Garlic Festival.
Cikin sanarwar shugaba Buhari ya kara da cewa, Najeriya za ta ci gaba da mutanta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, "ba tare da yin la’akari da wanda yake shugabanci ba."
Hukumomin Kamaru sun ce mayakan ‘yan aware sun karbe ikon sama da makarantu 50 a yankin rainon Ingila, lamarin da ake ganin zai iya mayar da hannun agogo baya, a kokarin da gwamnati ke yi na farfado da harkar ilimi a yankin a watan Satumba.
Sai dai duk da haka, ‘yan majalisa daga jam’iyyar Republikan ta Trump, sun yi hasashen cewa ba za’a samu wasu bayanan da suka wuce wadanda aka ji a baya ba.
Birtaniya na shirin daukan matakin kan Iran saboda kwace mata jirgin dakon manta da ta yi a Mashigin Hormuz.
Wani harin da ake zargin dan kunar bakin ya kai a kofar shiga wani Otel da ke kusa da wata mahada da ake kira K-4 da ake yawan hadahada a Mogadishu ya hallaka mutum 17 tare da jikkata wasu da dama.
Ana sa ran jam'iyyar sabon shugaban kasar ta taka rawar gani a wannan zabi, inda akasin hakan zai tilasta mata kafa gwamnatin hadaka.
Kafofin yada labarai da dama, sun ce an samu mace-macen ne a jihohin Maryland, Arizona da Arkansas.
Gwamnatin ta Trump ta kaddamar da wani shiri na sake komawa duniyar ta wata a shekarar 2024 da nufin sauka a duniyar Mars a karon farko nan da shekarar 2033.
Jagororin kungiyar ta Shi’a, suna zargin cewa hukumomin sun hana likitoci su ga shugaban nasu, lamarin da ya sa lafiyarsa take ta tabarbarewa.
Domin Kari