A jiya Litinin Wani kwararre a Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a gudanar da binciken kasa da kasa kan "laifin cin zarafi da zalunci," da suka hada da kisan kiyashi kan 'yan tsiraru addinai da kuma kisan kare dangi ga 'yan adawa a shekarar 1980 da aka aikata a Iran.
A jiya Litinin ‘yan majalisar dokokin Amurka daga bangarorin biyu suka yi kira ga Daraktar hukumar tsaron farin kaya ta Amurka Kimberly Cheatle da ta yi murabus, yayin da take ba da shaida kan gazawar hukumar wajen hana yunkurin kashe dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donald Trump.
Membobin jam'iyyar da dama sun ce suna goyon bayan Harris a matsayin wacce zata maye gurbin Biden a jam'iyyar kuma wacce za tayi takarar shugabancin kasar tare da Trump. Sai dai wasu sun ce suna bukatar jam'iyyar Democrat ta yi zabben fidda da gwani a babban taron jam'iyyar na wata mai zuwa.
Shugabannin duniya sun fara bayyana ra’ayoyin su bayan shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da janyewa daga takarar shugabancin kasar a jiya Lahadi.
Muhimmancin babban taron RNC a tsarin zaben Amurka; Shugaba Joe Biden ya gabatar da jawabi na musanman inda ya bukaci Amurkawa da su hada kai, su guji tashe-tashen hankali na siyasa; Tarihin tashin hankali a siyasar Amurka da wasu rahotanni
Malawi ta sanar da cewa, ta kawo karshen barkewar cutar kwalara mafi muni a kasar, cutar da ta kashe kusan mutane 2,000 tun bayan bullar ta a watan Maris din shekarar 2022.
Domin Kari