Shugabannin kasashen Afirka dabam-dabam sun hallara a New Delhi, babban birnin Indiya, domin taron kolin da kasar ta kira da kasashen Afirka.
Hotunan Taron Kolin Kasashen Afirka Da Kasar Indiya A Birnin New Delhi

10
Shugaba John Dramani Mahama, na Ghana tare da maidakinsa, Lordina, a lokacin da karamin ministan Noma na Indiya, Mohanbhai Kundariya ke tarbarsu.

11
Karamin minista a gwamnatin Indiya, G M Siddeswara yana tarbar shugaba Ellen Johnson Sirleaf, ta kasar Liberiya.

12
Mataimakin shugaban kasar Tanzaniya, Mohammed Gharib Billal, a hagu, yana gaisawa da karamin ministan man fetur na Indiya, Dharmendra Pradhan, lokacin da ya isa wurin taron kolin.

13
Wani karamin minista a gwamnatin Indiya, Rajyavardhan Singh Rathore, yana tarbar shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe a lokacin da ya isa wurin taron kolin.