Wani hari ta sama da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira a yankin Tigray na arewacin kasar Habasha ya kashe 'yan gudun hijirar Eritriya uku.
Asibitoci a duk faɗin Amurka suna jinkirin aikin fida na tiyata don samar da isassun ma'aikata da gadaje saboda hauhawar cutar COVID-19 nau’in Omicron dake yaduwa.
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ma’aikata ‘yan kasar China uku da ke aikin gina madatsar ruwa dake tsakiyar Najeriya, tare da kashe wasu ma’aikatan guda biyu 'yan Nigeria, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Alhamis.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta kara jaddada aniyar ci gaba da bibiyar shari’ar nan ta mutanen da ake zargi da handame kudaden makamai a ma’aikatar tsaron kasar bayan bayyanar wasu takardun dake nunin hukumomin Nijar sun janye daga wannan shari’a.
A Najeriya sarakunan gargajiya sun jima suna korafi akan ba su da wani tanadi na aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su wanda za su bayar da gudunmowa ga ci gaban al'umar kasa.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta gabatar da wasu mutane da ta kama dauke da kilogram (kg) sama da 200 na hodar iblis da aka loda a motar magajin garin Fachi dake jihar Agadez a Nijar a lokacin da suka yi kokarin ketarawa zuwa kasar Libya.
A Najeriya, alamu na nuna cewa akwai yiwuwar a samu saukin matsalolin rashin tsaro a wasu yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga saboda a baya bayan nan ana jimawa ba tare da an kai hari ba a wasu wuraren, sai dai kuma ana fuskantar kananan hare-hare a wasu wurare dabam.
Masarautar Bauchi da ta Dass a Najeriya sun bukaci gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Bauchi su kafa wani kwamiti da zai binciko matasan da suka ci mutuncinsu a makon da ya gabata.
Hukumomi a Afirka ta Kudu sun ce an samu nasarar shawo kan wutar da ake zaton wani mutun ne ya kunnata wacce ta kone ginin majalisar dokokin kasar, bayan gobarar ta shafe kwanaki biyu ta na tafka barna.
A cikin shirin na wannan makon a jamhuriyar Nijar shekarar 2021 cike take da kalubale ga ‘yan kasar da dama. Wasu mazauna kasar suna da kyakkyawar fata a game da yadda shekarar 2022 za ta kasance, da wasu rahotanni
Lauyar dake kare ‘yan Rwandar nan da gwamnatin Nijar ta kora daga kasar ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira rashin mutunta alkawuran da kasar ta dauka a yarjejeniyar da suka cimma da MDD akan batun bai wa wadanan mutane mafaka.
A Najeriya daidai lokacin da shekara ta 2022 ke dab da shigowa wadda ita ce jajibirin shekarar zabubuka a kasar, alamu na nuna wankin hula na neman kai dare ga jam'iyar APC mai mulkin kasar domin ta kasa sasanta rikice-rikice da ke ci gaba da tarwatsa ta.
Sama da sarakuna dari da goma sha uku ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu a sassa daban-daban na Najeriya cikin shekaru hudu da suka shige. Yayin da kuma wasunsu ma suka rasa rayukansu hade da hadimansu.
Dattawa da masana a jihar adamawa sun mikawa Majalisar Dokokin jihar kudirinsu na nuna rashin amincewa da kudirin Majalisar na kirkiro wasu masarautun gargajiya da suka hada da Hakimai da kuma masu jimillu hade dama kara wasu gundumomi a jihar.
Hukumomin jamhuriyar Nijar sun kori wasu ‘yan Rwanda daga kasar saboda dalilan da aka bayyana a matsayin na diflomasiya, sai dai wasu ‘yan rajin kare hakkin dan adam na ganin alamar keta hakkin dan adam a wannan lamarin.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a duniya ya karu da kashi 11 cikin 100 a makon da ya gabata idan aka kwatanta da satin da ya wuce, inda nahiyoyin Amurka ne aka fi samun karin.
Kungiyoyin ‘yan kasuwar Jamhuriyar Nijar sun bayyana farin ciki bayan da shugaban hukumar Douane ya umurci ma’aikatansa su dakatar da matsawa ‘yan kasuwa game da takardar izinin wucin gadin fiton kaya.
Jama'a na ci gaba da shiga kunci sanadiyar ayyukan ‘yan bindiga da ke ci gaba da aika- aikar su a jihohi da dama na arewacin Najeriya.
Yayin da a ke haramar shiga sabuwar shekara ta 2022, ‘yan Najeriya na nuna matukar damuwa kan shirin gwamnati na janye dukkan tallafin man fetur da hakan zai sa lita ta kai Naira 320-340 daga Naira 162.
Domin Kari