Turner ta rasu ranar Talata, bayan doguwar jinya a gidanta dake Küsnacht kusa da Zurich, a cewar manajanta. Ta zama 'yar kasar Switzerland ne shekaru goma da suka wuce.
Rikicin Sudan da ya sa aka rufe sararin samaniya ya janyo karin kudin kujerar aikin Hajji a Najeriya da dala 250, don dole a zagaya ta hanya mai nisa da hakan ya sa kamfanonin jiragen da za su yi jigilar maniyyatan suka bukaci karin kudi.
Kuma tuni an mika dokar ga shugaban kasa domin ya rattaba mata hannu ta zama doka. Daga dukan alamu dokar ta samu karbuwa domin ‘yan majalisar sun ce dokar ba ta su ba ce.
A yanzu haka dai filin saukar jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Minna fadar gwamnatin jihar Nejan Nigeria na cikin wani yanayi na fitar hayyaci.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a wani taro da shugabannan jami’an tsaro a jihar, don sake duba matakan tsaro a karamar hukumar Mangu, ya ce, sun fahinci cewa akwai wadanda aka chapke da zargin hannu a rikicin.
Duk da barazanar da mabiya shi'a su ka yi na bijirewa rushe wasu gine-ginen mabiya shi'ar da gwamnatin jiha Kaduna ta yi, gwamnatin ta ci gaba rushe-rushen a wasu sassan jihar.
Zaben dai ya samu fafatawa da matasa inda a ka samu wasu daga cikin su ma sun lashe zabe musamman a majalisun dokoki.
Wani mazaunin jihar Kano a Arewacin Najeriya wanda a baya ya yi ta’ammali da miyagun kwayoyi, yanzu ya tuba, kuma har ya shiga taimakawa sauran masu ta’ammali da miyagun kwayoyin don ganin su ma sun daina, da wasu rahotanni
Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta kulla yarjejeniyar aiki da wasu kasashen Afirka don kara tunkarar yanayin tsaro a Gabar Tekun Guinea.
A shirin da ya bagata mun karbi bakuncin wadansu zaurawa a kasar Kamaru domin nazarin tasirin mutuwar aure ga ma’auratan musamman mata da ‘ya’yansu, da kuma yadda lamarin ya shafi ci gaban iyali.
A kashi na farko na wannan hira da Mansour ya yi mana bayani dangane da yadda aka yi ya tsinci kansa a halin nakasa.
Zababbun ‘yan majalisar dokokin Najeriya na ci gaba da kalubalantar matakin jam’iyyar APC mai mulki, kan wadanda za su shugabanci majalisun dokokin kasar na 10.
Yankin Sahel na Afirka ya zama wurin da ake fama da mummunan tashin hankali, amma rundunar hadin gwiwa da aka kafa a shekarar 2014 domin yakar kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar IS da al-Qaida da sauran su, ta kasa dakile kutsen da suke yi.
Shin wadanda su ka lashe zabe za su cika alkawarin kyautata rayuwar matasa ko sun yi zane kan ruwa ne, matasan sun duba matakan dogaro da kai maimakon jiran gawon shanu.
Domin Kari