Matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Najeriya; a Ghana kuma rashin samun gonaki na daga cikin matsalolin da mata masu sha’awar yin noma ke fuskanta, da wasu rahotanni
A cikin shirin na wannan makon, rashin ayyukan yi ko jarin tsira kasuwanci wata matsala ce da ke daga hankulan masu bukata ta musamman a Ghana.
Wata tawagar daliban Najeriya da ke tserewa rikicin Sudan ta yi nasarar shiga kasar Masar kamar yadda ofishin jakadancin Najeriya ya tabbatar a ranar Talata.
Bayan kusan mako biyu ana musayar wuta tsakanin sojojin Sudan da rundunar kai daukin gaggawa ta kasar-RSF, bangarorin biyu sun sanar da tsagaita wuta a ranar Talata. Sai dai an ci gaba da samun ‘yan hare-hare, da wasu rahotanni
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin tankar man fetur a mahadar hanyar Bauchi, dake nan cikin garin Jos.
Hukumar Alhazan dai ita ce ke da alhakin kai maniyyata aikin Hajji a kasa mai tsarki ta Saudiyya domin sauke farali, da kuma mabiya addinin Kirista da ke zuwa kasar Isra’ila domin yin ta su ibadar.
Bankin Duniya ya ce Najeriya na cikin wani yanayi mai rauni tun shekaru biyu da suka wuce, lokacin da aka samu tashin farashin mai a karshen shekara 2021.
A cikin shirin na wannan makon; a makon da ya gabata shirin ya sauka a jihar Agadez dake yankin arewacin jamhuriyar Nijar inda a kashi na farko muka tattauna da shugaban kungiyar nakasassu na jihar Abdou Moutsallabi.
Shugaban wata kungiyar asiri a Kenya ya shaida wa mabiyansa duniya za ta kare a ranar 15 ga watan Afrilu, ya umarce su da su kashe kansu da yunwa domin su kasance na farko cikin wadanda za su je aljanna, kamar yadda wani ‘dan uwan mabiyan kuma ma’aikacin asibiti ya shaida wa Reuters a ranar Laraba.
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnati na daukar matakan dawo da ‘yan Najeriya gida don kauce wa rikicin Sudan ta hanyar kasar Masar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada muhimmanci aiwatar da taron ƙolin ƙasashen yankin tekun Guinea wato "Gulf of Guinea Commission" mai fafutukar kare yankin daga ayyukan masu fashin teku.
Tsadar filawar alkamar a Ghana wacce ta haifar da tashin farashin biredi ta sa wasu masu sana’ar biredin komawa amfani da rogo da ake nomawa a kasar, da wasu rahotanni
Domin Kari