Birgediya Janaral Tukur Isma'il Gusau, sabon kakakin hedikwatar rundunar tsaron Najeriya, ya amshi ragamar aiki daga hanun darakta mai barin gado, Manjo Janaral Jimmy Akpor.
A cikin shirin na wannan makon mun yi magana ne akan cututtukan da suka shafi cikin ciki da hanjin ‘dan adam.
Yayin da mahukunta a Najeriya ke kokarin yakar ‘yan ta'adda, su kuwa ‘yan ta'addan sai kara samun kwarin gwiwa suke yi na kara kai sabbin hare-hare.
A Jamhuriyar Nijar kwamitin da aka dora wa alhakin nazarin hanyoyin magance matsalolin da ke dabaibaye ayyukan majalisar sansanta rigingimun syasa wato CNDP ya gabatar da rahotonsa a zaman da ya hada bangarorin siyasa da yammacin jiya Laraba.
Ana zargin shugaban 'yan adawar kasar Senegal, Ousmane Sonko ne da fyade da yin barazanar kisa ga wata ma'aikaciyar salon din kwalliya a shekarar 2021, kamar yadda wani alkali mai bincike ya bayyana a wata wasika.
Yau Laraba wani jirgin sama mai saukar ungulu a wajen babban birnin kasar Ukraine, ya kashe mutane akalla 15, ciki har da ministan harkokin cikin gida Denys Monastyrsky.
A cikin shirin na wannan makon, bangare ne na karshe da ya duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar marabtar baki, kyautata makwabta, tallafawa marayu da sauran su.
A wani mataki na farfado da kuma inganta bangaren ilimi a Jihar Zamfara, gwamna Bello Matawalle ya amince da shawarwarin masu ruwa da tsaki na bangaren ilimi na daukan sabbin malamai 412.
Sa'o'i kadan bayan da kamfanin NNPC ya bada sanarwar samun Man fetur a Jihar Nasarawa da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun bada ra'ayoyi mabanbanta a game da al'amarin.
Wani hatsarin jirgin sama ya kashe mutane akalla 68, a cewar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Nepal.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun yanke shawarar rufe wasu kasuwanni a kauyuka da dama na Jihohin Tilabery da Tahoua, da nufin toshe hanyoyin da ‘yan ta’addar arewacin Mali ke amfani da su wajen samun kudaden shiga.
A arewacin Kenya, gwamnati da kungiyoyin agaji sun kaddamar da wani shiri na koyar da ilimi mai zurfi na kwamfuta ga makiyaya domin su samu ayyukan yi masu dorewa, da wasu rahotanni
An yi kira ga 'yan takarar da su rika sanya ido akan wadanda suka nada a mukamai domin su tabbatar da cewa sun rike amana.
Wata sabuwar dambarwa ta taso a Jamhuriyar Nijar tsakanin ‘yan adawa da masu mulki bayan da shugaban Jam’iyar RDR Canji Alhaji Mahaman Ousman ya bai wa matarsa mukamin sakatariya a ofishinsa na tsohon shugaban kasa.
A cikin shirin na wannan makon mun yi magana ne akan tsarin iyali domin bada tazarar haihuwa, mai kula da marasa lafiya da kuma ungozoma.
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), jiya Laraba ta ce tana kira ga kasar China, da ta yi karin bayani kan yaduwar da cutar COVID-19 ke yi a kasarta.
Ganin yadda Malamai kan ba da mabanbantan fatawoyi kan aikin hajji, ya sa hukumar kula da aikin hajji da zuwa Jerusalem ta Jihar Kaduna fitar da sabbin tsare-tsaren aikin hajji ga maniyyata a wannan shekara ta 2023.
Bayan wata mahaukaciyar guguwar da ta yi kaca-kaca da wasu yankunan California a Amurka, ana ta yunkurin shara tare da gyara barnar da ta yi a ranar Laraba, yayin da aka samu saukin saukar ruwan sama a yankuna da dama.
A cikin shirin na wannan makon mun ci gaba ne da wanda mu ka fara a makon jiya da ya duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar marabtar baki, kyautata makwabtaka, tallafawa marayu da sauran su.
Akalla mutane 40 ne suka mutu inda wasu 87 suka jikkata bayan da wasu motocin bas guda biyu suka yi karo a kusa da Kaffrine a tsakiyar kasar Senegal.
Domin Kari