A ranar Litinin ne wata kotun manyan laifuka ta Ikeja ta yanke hukuncin daurin shekaru 21 ga wani mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, mai suna Evans, bisa samunsa da laifin yin garkuwa da wani dan kasuwa Slyvanus Ahamonu, tare da karbar $420,000 a matsayin kudin fansa daga iyalansa.