A Jamhuriyar Nijar, jiya Alhamis, 15 ga watan Satumba, aka yi shagulgulan baje kolin al’adun al’ummar Tubawa bayan da a shekarar 2020 shugabanin wannan kabila dake zaune a kasashen Nijar, Libya, da Chadi suka yanke shawarar ware ranar.
Gwamnatin Ghana ta gurfanar da wasu 'yan kasar China su hudu ciki harda shahararriyar mai hakar ma'adinai a Ghana, Huang Ruixia, da aka fi sani da Aisha Huang, a gaban babban kotun Accra.
A kalla Mutane hudu sun mutu sakamakon wani hatsarin Jirgin ruwa a babban kogin Binuwai da ya ratsa karamar hukumar Ibbi dake Jihar Taraba. Jirgin mai daukar mutane ne da kuma motocinsu zuwa kasuwannin kauyukan da ke ci mako-mako a yankin na karamar hukumar Ibbi.
A Najeriya alamu na nuna cewa duk fafatukar da hukumomi da wasu kungiyoyi ke yi wajen hana shan miyagun kwayoyi, har yanzu da sauran aiki gaba.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake kai ziyara Jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar don kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ta kammala, duk da barazanar 'yan aware.
Jami’ai a Nijar sun bullo da wata fasaha ta yin amfani da jirgin sama wajen harbin giza-gizai domin samar da ruwan sama, da wasu rahotanni
A yayin da ake ci gaba da nuna alhini kan mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta II a fadin duniya, ba a bar Najeriya a baya ba inda wasu jiga-jigai a kasar suka yi ta bayyana irin yadda suke jimamin mutuwarta, tare da ambata irin tasiri da marigayiyar take da shi a duk duniya.
Masanin kimiyyar siyasar duniya na jami’ar Bayero ta Kano Dr. Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce kasashen Afurka da dama za su yi juyayin mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu don rawar da ta taka wajen karbar ‘yancin su.
Harkokin tattalin arziki, cinikayya da zamantakewa na ci gaba da gurguncewa a sassan kananan hukumomin dake yankin kudancin Jihar Jigawa saboda karyewar gadojin dake kan titunan yankin biyo bayan ambaliyar ruwa.
Ko talakawa za su fito zaben 2023 na Najeriya dake gabatowa?
A ci gaba da laluban hanyoyin shawo kan matsalar tsaro a yankin Arewancin Najeriya dama take hakkin bil’adama, cibiyar samar da zaman lafiya da diflomasiyya da ci gaban al’umma ta Jami’ar Maiduguri ta gudanar da bincike da ya kai ga wallafa littatafai biyu.
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta rasu ta na da shekaru 96. Ita ce sarauniya mafi dadewa a kan karagar mulki a duniya kuma a bana ne ta yi bikin cika shekaru 70 a kan karagar mulki. Mun yi waiwaye kan rayuwarta, kasancewa daya daga cikin shugabannin da aka yi a duniya da ake matukar girmamawa
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya shiga jerin shugabanin ‘kasashen duniya a gurin aikewa da sakon ta’aziyya ga mahukuntan Ingila akan rasuwar sarauniyar Ingila, Elizabeth ta Biyu.
Masana kimiyyar siyasa na bayyana cewa kalubalen tattalin arziki da matsalolin da ta gada daga gwamnatin Boris Johnson, su ne mafi girma dake gaban sabuwar Firai Ministar Burtaniya Liz Truss.
Kungiyar mafarauta ta hadin gwiwa ta kashe ‘yan bindiga sama da shirin a dajin yankin Bali da Gossol a Jihar taraba, sun kuma tarwasta sansanin ‘yan bindigan da suka hana mazauna yankin zaman lafiya.
Domin Kari