Gabanin a kai ga cimma wannan matsaya, an kwashe watanni ana jerin zanga zanga, wadanda suka faro tun daga watan Disambar bara, kan tsadar farashin man fetur.
Imran Khan ya ce ranar samun ‘yan cin kai wata dama ce da za mu nuna farin cikinmu, amma yau muna cikin bakin ciki na yanayin da ‘yan uwanmu na Yankin Kashmir da aka mamaye a Jammu da kuma Kashmir wadanda India take cin zalinsu.
Dan shekaru 66 da haihuwa Epstein yana fuskantar shari’a kan tuhume tuhuman gwamnatin tarayya na safarar mata da ake lalata da su da ya hada da yara mata kanana da wasunsu shekarun su bai gaza goma 14.
Za a fara gasar a ranar 26 ga watan Oktoban bana inda Brazil za ta karbi bakuncin gasar.
Wannan karon a taron, sun maida hankali kan rawar da matasa Krista za su taka a ci gaban kasa, da kuma yadda za su kauce ma shiga kungiyoyin ta'addanci.
An kammala zaman da aka kwashe kwanaki 9 ana yin sa a Qatar da goshin Asuba a yau Litinin, a cewar wani dan kungiyar ta Taliban.
Tun da farko dama, gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, ta yi na’ama da wannan matsaya da aka cimma domin a samu a yi bubkuwan salla da za a fara a gobe Lahadi.
A wani sakon taya Musulman Najeriya murnar wannan rana, shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’umar musulman kasar da su rika nuna halayen da sauran jama’a za su rika dora koyarwar addinin Islama akan mizani mai kyau.
A ranar Litinin din da ta gabata, Amurka da Korea ta Kudu suka fara atisayen, wanda ake shirin kammala shi a ranar 20 ga watan nan na Agusta.
A kasashe masu tasowa, jama'a kan dunguma wajen diban mai a duk lokacin da motar dakon mai ta fadi.
Shi dai aikin hajji, yana daya daga cikin shika-shikan musulunci da ake so Musulmi ya yi, ko da sau daya ne a rayuwa, idan dai yana da hali da kuma koshin lafiya.
Mai magana da yawun Ministan Harkokin Cikin Gida na Afghanistan, Nasrat Rahimi ya ce, dan kunar bakin waken ya tayar da motar da aka makareta da boma boman a lokacin da jami’an tsaron suka tsayar da shi a wani wurin duba ababan hawa a wajen ofishin ‘yan sandan.
Shugaban Donald Trump ya kai ziyara tare da mai dakinsa, don jinjinawa wadanda suka fara kai daukin farko da kuma tattunawa tare da iyalai da suke zaman makoki da wadanda suka tsira daga wannan bala’in.
Lauyoyin El Zakzaky, sun nemi kotun ta ba shugaban mabiya Shi’ar damar ya je kasar waje neman magani da shi da mai dakinsa Zeenat, saboda rashin lafiya da suke fama da ita.
“Ina mai farin cikin rattaba hannu a wannan kwantiragi na zuwa wannan mashahuriyar kungiya.” In ji Maguire, bayan da ya kammala komawa kungiyar ta United.
Ana fatan, kwana guda bayan rattaba hannun, za a ayyana majalisar mulkin gwamnatin ta wucin gadi, wacce za ta tafiyar da ragamar mulkin kasar har na tsawon shekaru uku.
Kasashen Turkiyya da Rasha ne suka hada kai aka cimma wannan matsaya ta tsagaita wuta, abin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yaba. A daren ranar Alhamis ake fatan shirin zai fara aiki.
Wannan hari na baya-bayan nan, na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan wani harin kan-mai-uwa-da-wabi, da aka kai a garin El paso da ke jihar Texas, a kantin sayar da kayayyaki na Walmart, inda mutum 20 suka mutu kana wasu 26 suka jikkata.
“Rundunar ‘yan sandan, tana gargadi ga masu shirya wannan zanga zanga da masu marawa kungiyar Global Coalition for Security and Democracy baya, da su yi watsi da wannan gangami da suka shirya.”
Domin Kari