Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Kaita yayi maraba da takwaransa sabon shugaban kasar faransa Emmanuel Macron a wata ziyara ta farko da yayi zuwa ga rundunar sojojin faransa dake kasar Mali su 4000 (Shiya Barkhane) dake cikin kasashe biyar dake yakar yan ta'addan yankin Sahel.
Hotunan Ziyarar Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron A Gao Dake Mali

1
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kaiwa dakarun sojan Faransa ziyara a Gao dake arewacin Mali, ranar Juma'a 19 ga watan Mayu shekarar 2017.

2
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci sojojin Faransa na Operation Barkhan, wadda ta zama rundunar soji mafi girma bayan Faransa a waje dake Gao, arewacin Mali, ranar Juma'a 19 ga watan Mayu shekarar 2017.

3
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya tattauna tare da 'yan jarida a jihar Gao dake arewacin Mali, ranar Juma'a 19 ga watan Mayu shekarar 2017.

4
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa a jihar Gao dake arewacin Mali a wata ziyara zuwa ga rundunar sojojin Faransa dake kasar, ranar Juma'a 19 ga watan Mayu shekarar 2017.
Facebook Forum